Daliban Najeriya sun samu shafin korafi akan cin zarafi

Daliban Najeriya sun samu shafin korafi akan cin zarafi

- Duba da yawaitar cin zarafi ko lalata da dalibai da ya yawaita a manyan makarantun Najeriya, an bude shafin kai korafi akan hakan

- Dan takarar shugaban daliban Najeriya, Sunday Asefon ya bude shafin kai korafi akan mummunan aika-aikar

- Dan takarar ya ce, matukar aka zabeshi, zai tabbatar da an wallafa sunayen tare da mika sunayen malaman da abun ya shafa don ladaftar dasu

Sakamakon yawaitar cin zarafin dalibai mata da ake a manyan makarantun Najeriya, dan takarar kungiyar shugaban daliban Najeriya, Sunday Asefon, ya bude shafi a yanar gizo na kai korafin cin zarafin da malaman manyan makarantu ke yi wa dalibai.

Asefon, dalibi ne a jami'ar jihar Ekiti, Ado-Ekiti, ya yi alkawarin wallafa rahoton matukar ya zama shugaban daliban Najeriya.

KU KARANTA: Wani dan bindiga ya budewa mabiya addinin kirista wuta a cikin coci

https://bit.ly/2OBwzFx na cikin takardar da babban mataimaki na musamman gareshi akan yada labarai, Pelumi Fasogbon ya bawa manema labarai a ranar Asabar.

Asefon, kamar yadda takardar ta sanar, ya ce sabuwar fasahar makami ce ta fallasa duk wani malamin jami'ar wanda sunansa ya bayyana a ciki.

Ya bukaci duk daliban da aka ci zarafi ko aka yunkurin cin zarafi da su sa hannu don za a mika su ga FIDA, ICPC, NUC, ASUU tare da duk kwamitin zartarwar jami'o'i.

Kamar yadda dan takarar ya sanar, gurfanar da malaman da abin ya shafa zai biyo baya amma hakan zai danganta da nauyin laifinsu da aka binciko.

"Idan na zama shugaban dalibai, zan tabbatar da an dawo da tarbiyyar karartu a cikin manyan makarantu."

"Rijistar na nan a yanar gizo kuma zamu fallasa duk wanda sunansa ya bayyana fiye da sau daya. Lokacin lalata ko cin zarafin dalibai ya wuce," Afeson ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel