Tsoffin soji masu murabus sun bukaci gwamnatin tarayya da ta kafa musu ma'aikatarsu

Tsoffin soji masu murabus sun bukaci gwamnatin tarayya da ta kafa musu ma'aikatarsu

- Tsoffin sojin Najeriya masu murabus sun bukaci gwamnatin tarayya da ta kafa musu ma'aikatarsu

- Gogaggun sojin sun ce hakan zai sa su bayyana baiwar da suka mallaka

- Sun jaddada cewa zasu taka rawar gani wajen ganin cigaban tsaro da habakarsa a kasar nan

Tsoffin sojoji masu murabus a kasar nan sun nemi gwamnatin tarayya da ta kafa musu ma'aikata cikakkiya da zata kula da walwalarsu.

Masu murabus din sun yi kiran ne a takardar da suka ba manema labarai a Abuja bayan kammala taron kungiyar gogaggun soji.

Sun kara da kiran gwamnati da ta basu damar bayyana baiwar da suke da ita.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da ranar fara rijistar maniyyata

Gogaggun sojin sun yanke shawarar aiki karkashin inuwa daya mai suna "Kungiyar gogaggun sojojin Najeriya".

Sun yi alkawarin biyayya ga gwamnati kuma a shirye suke don bada gudummawarsu ga tsaron kasa da cigaban ta.

Kamfanin dillancin labarai ya tunatar cewa, an bude taron ne a ranar Alhamis India shugaban jami'an tsaro, Janar Abayomi Olonisakin, ya jaddada cewa akwai bukatar hada kan gogaggun sojojin Najeriya.

Ya yi kira ga taron, da su kafa kwamitin wucin gadi don fara hadin kan tare da kirkiro da "Kungiyar gogaggun sojin Najeriya".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel