Ololoye: Duk da alkawarin da Buhari ya yi, Gwamnati ba ta da niyyar kara albashi

Ololoye: Duk da alkawarin da Buhari ya yi, Gwamnati ba ta da niyyar kara albashi

Shugaban kungiyar TUC na ‘Yan kasuwan Najeriya, ya yi hira da wani ‘Dan jarida Olufemi Atoyebi kwanan nan inda ya bayyana masa raunin gwamnati wajen dabbaka tsarin sabon albashi.

Quadri Olaleye yake nuna cewa gwamnatin da Muhammadu Buhari ya ke jagoranta tayi wa ma’aikata alkawarin kara albashi ne amma ya ke cewa babu abin da ke nuna da gaske ta ke yi.

Mista Olaleye ya bayyana cewa gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan N30, 000 a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya zai kashewa ma’aikata karfin gwiwar aiki a daidai wannan mara.

Shugaban kungiyar ta TUC yake cewa duk da wa’adin da aka sa na zama tsakanin gwamnati da ‘Yan kwadago, har gobe babu wani taro da aka kira tsakanin gwamnati da bangarensu tukuna.

Olaleye yake cewa a Ranar 15 ga Oktoba ne su ke sa ran cewa za su yi zaman gemu da gemu da gwamnati. Wakilin ma’ikatan ya tabbatar da cewa su na nan a kan matsayar da su ke kai tun tuni.

KU KARANTA: Sanatoci sun ce akwai matsaloli a dunkule cikin kasafin da Buhari ya kawo

Kungiyoyin kwadago su na so a kara albashin ma’aikatan da ke kan mataki na 07 zuwa na 14 da 29%, yayin da su ka nemi a karawa masu rukuni na 15, 16 da kuma 17 kashi 24% a kan albashinsu.

Gwamnatin Kasar ta ki yin na’am da wannan inda ta fara maganar karin 4%, yanzu dai gwamnati ta motsa zuwa 11%. Ololeye ya koka da dabi’ar Wakilan gwamnati na nuna iko a wajen zamansu.

“Rashin cika alkawarin gwamnatin tarayya ne ya kawo mu wannan matsayi. Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kara albashi, amma Wakilansa ba su da niyyar yin hakan.”

Shugaban na TUC ya zargi jami’an gwamnatin da su ke zama da su da cewa ba su da niyyar cika wannan alkawari inda ya roki shugaban kasan ya sa baki tun kafin yarjejeniyar ta jagwalwgwale.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel