Mutane 12 sun mutu bayan 'yan bindiga sun bude wuta a kan Masallata a Masallaci

Mutane 12 sun mutu bayan 'yan bindiga sun bude wuta a kan Masallata a Masallaci

Wasu 'yan bondiga dauke da makamai daban-daban sun kai hari hari a wani Masallaci tare da kashe Masallata a kalla 12 a kasar Burkina Faso, kamar yadda kakafen watsa labaran cikin gida a kasar suka wallafa.

'Yan bindigar sun kai harin ne wani babban Masallaci da ke kauyen Salmossi da ke gabashin kasar da yammacin ranar Juma'a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.

Wata majiyar AFP ta sanar da ita cewa mutane 13 ne suka mutu nan take bayan 'yan bindigiar sun bude wuta a kan Masallatan. Kazalika, majiyar ta ce wasu mutane biyu da suka samu raunuka na ciki mawuyacin hali.

"Tun safe mutane ke barin yankin da aka kai harin," a cewar wani mazaunin garin Gorom-Gorom mai makwabtaka da Salmossi

"Duk da an kawo sojoji bayan an kai harin, hakan bai kwantar da hankalin jama'a ba, saboda sun cigaba da barin yankin," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Abin da Aisha Buhari ta fada bayan dawowar ta Najeriya

Wata majiya daga cikin jami'an tsaro a kasar sun sanar da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an kashe mutane 15 yayin harin.

Har yanzu ba a san su waye 'yan bindigar da suka kai harin ba.

Ana zrgin 'yan bindigar da ke kashe mutane a Burkina Faso da shigo wa kasar daga kasar Mali tare da ingiza rikicin addini, musamman a arewacin kasar.

Kasar Burkina Faso na fuskantar yawaitar kai hare-hare, wadanda ake alakanta wa da kungiyar al-Qaeda da kuma IS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel