Yanzu Yanzu: Aisha Buhari ta baro Ingila, tana a hanyar dawowa Najeriya

Yanzu Yanzu: Aisha Buhari ta baro Ingila, tana a hanyar dawowa Najeriya

Uwargidar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta baro kasar Ingila, a yanzu haka tana a hanyar dawowa gida Najeriya.

Uwargidar jakadan Najeriya a kasar Ingila, Misis ModupeOguntade ce tayi mata rakiya a yayinda zata baro kasar.

Aisha ce ta bayyana wannan jawabii a shafinta Twitter a yammacin ranar Asabar, 12 ga watan Oktoba.

KU KARANTA KUMA: Kasafin 2020: Aso Rock za ta kashe miliyan 18.5 kan abinci da sama da miliyan 45 kan fetur

An tattaro cewa ta kwashe tsawon makonni da dama bata kasar.

A baya mun ji yadda aka yi ta yada jita-jitan cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai auri mata ta biyu. Anyi zargin cewa Shugaban kasar zai raya sunnah ne da Sadiya Umar Farouq, ministar kula da harkokin agaji da kare yaduwar annoba, a ranar Juma’a, 11 ga watan Oktoba.

Anyi ta yada jita-jitan cewa uwargidar Shugaban kasar ta dawo kasar domin nuna fushinta akan lamarin, amma sai na kewaye da Aso Rock suka rufe ta.

Sai dai hasashen ya zama karya bayan tabbatar da cewar uwargidar Shugaban kasar na a kasar Ingila, yayinda Sadiya Farouq ke a birnin New York a yanzu haka, inda take yada kamfen din majalisar dinkin duniya na yaki da talauci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel