Da dumi-dumi: Aisha Buhari ta dawo gida Najeriya (Hotuna)

Da dumi-dumi: Aisha Buhari ta dawo gida Najeriya (Hotuna)

- Aisha Buhari ta dawo Najeriya bayan shafe watanni uku tana hutu a kasar Ingila

- Balaguron da tayi ya janyo rade-rade da jita-jita a kan yiwuwar rashin jituwa tsakanin ta da mijinta

- Aisha ta mika godiya ta musamman ga mijinta, abokanta, iyalanta da masu mata fatan alheri saboda goyon baya da kwarin gwiwa da suke bata

First Lady, Aisha Buhari ta iso Najeriya a safiyar ranar Lahadi 13 ga watan Oktoba bayan shafe watanni uku ba ta kasar.

Uwargidan shugaban kasar ta bar Najeriya ne run farkon watan Augustan 2019 domin yin aikin Hajja a kasar Saudiyya sannan daga bisani ta wuce kasar Ingila.

Aisha ta dira a filin tashi da saukan jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja a cikin jirgin British Airways misalin karfe 4.30 na safe.

Mai magana da yawun ta, Suleiman Haruna ya tabbatar da dawowar ta.

Da dumi-dumi: Aisha Buhari ta dawo gida Najeriya (Hotuna)
Aisha Buhari yayin a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikwe bayan ta dawo daga Ingila
Asali: Twitter

Da dumi-dumi: Aisha Buhari ta dawo gida Najeriya (Hotuna)
Aisha Buhari yayin da ta dira filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja a ranar Lahadi 13 ga watan Oktoba
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zamfara: Sojoji sun kashe 'yan bindiga 100 yayin da suka yi yunkurin kai hari gonar tsohon gwamnan jihar

Sanarwar da ya fitar ya ce: "A safiyar yau, First Lady, Dr. Mrs. Aisha Muhammadu Buhari ta dawo gida Najeriya bayan hutu mai tsawo da tayi a kasar Ingila. Ta sauka a filin tashi da saukan jirage na Nnamdi Azikwe misalin karfe 4.30 na safe cikin jirgin Bristish Airways."

A yayin da ta ke amsa zantawa da manema labarai, Aisha Buhari ta ce tana farin cikin dawowa gida Najeriya.

Ta ce a shirye take domin cigaba da aikin inganta lafiya da walwalar mata da yara da sauran masu rauni a kasar.

Tayi amfani da damar domin mika godiyarta da mijinta, iyalanta da masu mata fatan alheri bisa goyon baya da kwarin gwiwa da suke bata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel