Malamin jami'a ya yiwa yarinyar yar shekara 13 fyade har lahira

Malamin jami'a ya yiwa yarinyar yar shekara 13 fyade har lahira

Babban malami a kwalejin fasahar jihar Benuwe, Ugbokolo Andrew Ogbuja, ya gurfana gaban kotu a Makurdi kan laifin fyade yar shekara 13 mai suna, Ochanya Ogbanje, har ta mutu.

Wannan gurfanar ya faru ne shekara daya bayan mutuwar yarinyar a ranar 17 ga Oktoba, 2018 sakamakon fyaden da malamin jami'ar da dansa, Victor, sukayi mata.

Malamin ya gurfana ne gaban Alkali Ityonyiman kuma ya musanta zargin da ake yi masa yayinda aka karanta masa laifukan.

Lauyan gwamnati, Mista P.M Ukande, ya bukaci kotu ta garkame malamin a kurkuku sannan ta sanya ranar hukuntashi tunda ya musanta zargin da ake yi masa.

Lauyan malamin, Mista Abel Onoja, ya bukaci kotun ta wajabtawa lauyoyin yarinyar gabatar da hujjojin likitocin da aka ambata kafin hukunta wanda ake zargi da laifi.

Daga karshe, alkalin ya dae karar zuwa ranar 14 ga Nuwamba, 2019.

KU KARANTA: Wani matashi ya hallaka kishiyar mahaifiyarsa a Nasarawa

A wani labarin daban, babbar kotun tarayya da ke Maitama ta sanya 16 ga watan Oktoba don sauraron shari'ar Maryam Sanda, matar da ake zarginta da kashe mijinta, Bilyaminu Bello.

Mai shari'a Yusuf Halilu ne ya dage sauraron karar.

Ana zargin Maryam ne da kisan Bilyaminu, marigayin mijinta kuma dan tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Bello Muhammad a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2017.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel