Oshiomhole: Shugabanin APC na jihohi za suyi wata muhimman taro

Oshiomhole: Shugabanin APC na jihohi za suyi wata muhimman taro

Dukkan shugabanin jam'iyyar APC na jihohi za suyi taro a birnin tarayya Abuja a ranar Lahadi domin tattaunawa kan matsalolin da ke tsakaninsu da shugabanin jam'iyyar na kasa.

A cewar The Punch, za ayi taron ne domin tattaunawa kan cigaban da aka samu bayan karewar wa'adin kwanaki 10 da aka bawa Kwamitin Gudanarwa karkashin shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomhole.

Kungiyar da shugabanin APC na jihohi a ranar 23 ga watan Satumba sun bawa Kwamitin Gudanarwar jam'iyyar wa'adin kwanaki 10 domin magance wasu korafe-korafe da suka gabatar.

Daga cikin muhimman korafe-korafen shine rashin bawa magoya bayan jam'iyyar mukamai a gwamnati da kuma rashin cike gibin wasu mukamai a jam'iyyar.

Har yanzu dai ba a maye gurbin sakataren jam'iyyar na kasa ba tun bayan da aka rantsar da Mai Mala Buni a matsayin gwamnan jihar Yobe.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An gano man fetur a yankin arewa maso gabas - NNPC

Shima mataimakin shugaban jam'iyya na kasa na yankin kudu, Niyi Adebayo ya zama ministan Masana'antu, Kasuwanci da Saka hannun jari.

Kazalika, Auditan jam'iyyar na kasa, Goerge Moghalu shima ya samu mukami a matsayin shugaban National Inland Waterways Authority kuma har yanzu ba a maye gurbinsa da wani ba.

Wa'addin da shugabanin na jihohi suka bayar ya kare kuma har yanzu shugabanin jam'iyyar na kasa ba su basu wata takamamen amsa ba.

Sakataren kungiyar kuma shugaban APC na jihar Enugu, Dakta Ben Nwoye, a ranar Juma'a ya tabbatar da taron da za ayi a ranar Lahadi.

Ya ce, "Eh, da gaske za muyi taro a ranar Lahadi kuma mun aike wa takwarorinsu goron gayyata.

"Dama mu kan yi taro lokaci zuwa lokaci domin yin bita kan cigaban da ake samu a jam'iyyar, saboda haka wannan ba sabon abu bane."

Ya kara da cewa, "Tabbas zamu tattauna kan wasikar da muka aike wa NWC. Za mu tattauna kan matakin da zamu dauka. Amma taro ne da kowa zai iya halarta, zamu cimma matsaya guda tare."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel