Gwamnan PDP mai matsayin Farfesa ya koma jami'a domin yin digiri a kan Shari'a

Gwamnan PDP mai matsayin Farfesa ya koma jami'a domin yin digiri a kan Shari'a

Gwamnan jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade, ya sake koma wa jami'ar tarayya da ke Calabar domin yin digiri na biyu (LLM) a tsangayar karatun shari'a.

Gwamnan ya fara halartar jami'ar domin daukan darasi a ranar Alhamis, inda har ya gabatar da aikinsa da aka bawa dukkan sauran daliban ajinsu.

Ayade ya nuna bajinta a fannin karatunsa na digir da digir-digir (PhD) inda bincikensa da nazari suka sa ya kirkiri wani inji mai amfani da hasken rana.

Gwamna Ayade ya fara karatunsa a wata makarantar firamare mai suna 'St. Stephens Primary School, da ke garin Obudu a jihar Kuros Riba. A garin Obudu Ayade ya kammala har karatunsa na sakandire.

Ya fara yin karatun digiri na farko a fannin karatun kananan kwayoyin hallittu da ba a gani da ido (Microbiology) a jami'ar Abrose Ali da ke Ekpoma a shekarar 1988. Ya yi karatun digiri na uku a jami'ar Ibadan a tsakanin shekarar 1990 zuwa 1994, inda ya samu kyauta da yabo a kan kwazon da ya nuna.

Ayade ya zama Farfesa tun yana da sauran kuruciyarsa.

Duk da kasancewarsa Farfesa, hakan bai hana shi cigaba da neman ilimi ba. Gwamnan ya koma jami'a tare da sake yin wani sabon digirin a bangaren ilimin shari'a inda ya kai ga zama kwararren lauya.

A ranar Alhamis, Ayade ya dauki darasi tare da sauran dalibai na tsawon sa'o'i hudu.

Daga cikin lakcarorin da zasu koyar da gwamna Ayade akwai, Jake Otu Enya, tsohon mamba a majalisar dokokin jihar Kuros Riba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel