Ramos ya kafa wani babban tarihi a kwallon kafan kasar Spain

Ramos ya kafa wani babban tarihi a kwallon kafan kasar Spain

Sergio Ramos ya kafa tarihi a tawagar kwallon kafan Spain inda ya zama dan wasan da yafi kowa bugawa kasar wasanni masu yawa. Ya buga wasanni 168 kenan yanzu inda ya sha gaba Iker Casillas wanda a da yake rike da kambun.

Ramos wanda shi ne kyaftin din Spain ya fito a cikin jerin sunayen ‘yan wasa da zasu fafata da kasar Norway a birnin Oslo. Wasan na daga cikin wasanni share fagen nema shiga gasar Euro ta 2020.

KU KARANTA:Dakarun sojin Najeriya sun ragargaji ‘yan Boko Haram wadanda suka kawo masu hari a sansaninsu

A shekara 14 da suka wuce ne Sergio Ramos ya fara bugawa kasar Spain wasa, a lokacin da kasarsa ta kara da China a wani wasan sada zumunta inda ta doke China da ci 3-0.

Bugu da kari, dan wasan mai shekaru 33 yanzu, yana daga cikin jerin ‘yan wasan da suka ciyowa Spain kofin duniya a shekarar 2010 a kasar Afirka ta Kudu da kuma kofin Euro a shekarar 2008 da 2012.

A shekarar 2016 ne ya amshi kambun kyaftin daga hannun Iker Casillas wanda ya bugawa Spain wasan karshe a shekarar.

A halin yanzu dai wasanni takwas kawai suka ragewa Ramos ya sha gaban wanda ke rike da kambun buga wasanni mafiya yawa a nahiyar tuari wato Gianluigi Buffon (176) dan kasar Italiya sai kuma wasa 16 ya rage masa ya kamo Ahmed Hassan wanda ya fi kowa a duniya da wasanni 184.

https://www.channelstv.com/2019/10/12/ramos-sets-spain-record-with-168th-cap/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel