Yadda yan bindiga suka kashe mutum 16 a wani harin masallaci

Yadda yan bindiga suka kashe mutum 16 a wani harin masallaci

Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga dake ikirarin jihadi sun kai farmaki wani masallaci a kauyen Salmossi dake kasar Burkina Faso a lokacin da mutane ke tsaka da sallah a ranar Juma'a.

An tattaro cewa mutane 16 ne suka rasa ansu a harin, inda suka tilasta wasu da dama tserewa daga kauyen da ke Oudalan kusa da iyakar kasar da Mali.

Wannan lamarin ya sanya kusan 1,000 da suka fusata hawa kan tituna a babban birnin kasar Ouagadougou domin nuna bacin ransu tare da yin Allah-wadai da kasancewar sojojin kasashen waje a yankin.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce sama da mutum 200,000 ne suka tsere daga gidajensu a Burkina Faso a cikin watanni uku da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Yadda uwa da yaranta su 3 suka mutu a lokaci guda

A makon da ya gabata ma 'yan bindiga sun kashe mutum 20 a wata mahakar gwal a yankin Soum mai makobtaka.

Hukumomin bayar da agaji na ci gaba gargadi kan karuwar hare-hare da kuma halin ni-'yasu da jama'a ke ciki a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel