Dakarun sojin Najeriya sun ragargaji ‘yan Boko Haram wadanda suka kawo masu hari a sansaninsu

Dakarun sojin Najeriya sun ragargaji ‘yan Boko Haram wadanda suka kawo masu hari a sansaninsu

Dakarun sojin Operation Lafiya Dole da na jami’an ‘yan sakai na farar hula sun ragargaji mayakan Boko Haram a unguwar Tungushe dake jihar Borno.

Channels TV ta ruwaito cewa mayakan na Boko Haram ne suka soma kai wa sojojin hari a sansaninsu dake unguwar inda sojojin suka mayar masu da martani ba tare da bata lokaci ba.

KU KARANTA:‘Yan sanda sun yiwa wani lauya dukan a kawo wuka a Anambra har sai da ya suma

Mayakan Boko Haram din sun yi kokarin dauke motar igwa guda daya ta sojojin, yayin da suka gamu da wasu sojojin a shiyar Gajiganna inda aka hana su wucewa da motar.

Majiyar da ta fito mana da wannan labarin ta ce babu hakikanin yawan mutanen da aka kashe a wannan musayar wutan tsakanin sojoji da ‘yan Boko Haram.

Manema labarai sun tuntunbi kakakin rundunar sojin Division 7, Kanal Ado domin jin yadda wannan al’amari ya auku, sai ya ce shi dai bai san komi game da faruwar wannan harin ba, a don haka ba shi da abinda zai ce.

A wani labarin mai kama da wannan kuwa, za ku ji cewa, Shugaba Buhari zai gana da Vladimir Putin domin samun karin karfin soji daga kasar Rasha.

Jakadan Najeriya a Rasha ne ya fitar da wannan labarin, inda ya ce, Buhari zai nemi sayen wasu kayan yaki da suka kama daga helikwafta, igwa, da dai sauransu.

https://www.channelstv.com/2019/10/12/troops-repel-boko-haram-attack-on-military-base-in-borno/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel