Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da ranar fara rijistar maniyyata

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da ranar fara rijistar maniyyata

- Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da al'ummar jihar ranar fara rijistar maniyyatan 2020

- Shugaban hukumar walwalar alhazai na jihar, Imam Hussaini Tsoho Ikara ne ya sanar da manema labarai a ranar Asabar

- Shugaban ya ce, za a fara rijistar ne a kananan hukumomi 23 na fadin jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ta ba maniyyata damar fara rijistar zuwa kasa mai tsarki don sauke faralin shekara 2020.

Yayin bayani ga manema labarai a ranar Asabar a garin Kaduna, Imam Hussaini Tsoho Ikara, shugaban hukumar walwalar alhazai ta jihar, ya ce gwamnatin jihar ta bada damar fara rijistar a kananan hukumomi 23 na fadin jihar.

KU KARANTA: Tubabbun 'yan ta'adda sun sako kansila, matarsa, 'yarsa da wasu mutane biyu

Ya ce, gwamna Nasir El Rufai ya bada damar ne bayan hukumar alhazai ta kasa ta bude fara rijistar maniyyatan shekara mai zuwa.

Ikara ya ce: "Muna bayani ne ga manema labarai don al'ummar jihar Kaduna su sani cewa, za a fara rijistar maniyyata a ranar 15 ga watan Oktoba,"

"Gwamnan jihar ya amince da a fara rijistar ne a kananan hukumomi 23 na fadin jihar." In ji shi.

Shugaban ya ce, za a iya fara biyan karanci N800,000 kuma yawan kudin shi ne N1.5m.

Kamar yadda ya ce, maniyyatan da suka biya sama da 1.5m za a dawo musu da na saman kudin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel