Wani dan bindiga ya budewa mabiya addinin kirista wuta a cikin coci

Wani dan bindiga ya budewa mabiya addinin kirista wuta a cikin coci

- A yau asabar ne wani dan bindiga ya budewa mabiya addinin kirista wuta a cikin coci

- Tuni dai 'yan sanda suka cafkeshi amma har yanzu ba a gano mutane nawa suka samu rauni ba

- Babbar majami'a ce da ke a birnin New Hampshire dake Amurka

Wani dan bindiga ya bude wuta a wata majami'a da ke Amurka.

Dan bindigar ya bude ma mutane wuta ne a wata majami'a da ke birnin New Hampshire Inda mutane da dama suka samu raunika.

'Yan sandan yankin sun gaggauta kama shi Inda suka yi awon gaba da shi.

KU KARANTA: Akwai yuwuwar barkewar cutar tetanus a jihohi 11 na arewacin Najeriya, UN

Wata jami'ar 'yan sanda a jihar arewa maso gabas ta sanar da jaridar AFP cewa bata san mutane nawa ne suka samu rauni a harin ba.

Hakazalika ta bayyana cewa bata san dalilin harbin ba.

Dan bindigar ya harbi mutanen ne a sabuwar majami'ar Fentacostal da ke Ingila. Farar majami'a ce da ke a babban kauye mai mutane a kalla 15,000 da ke kudanci.

Jami'ar 'yan sandan ta ce bata san ta yadda aka cafke dan bindigar ba don adana shi a wajen 'yan sanda.

Ba yau dai aka fara zuwa wajen bauta ba a kashe mutane.

A kwanakin baya an samu wani mabiyi addinin kirista da ya afkawa musulmai a masallaci Inda ya bude musu wuta. Mutane da yawa daga cikin masu bautar a ranar juma'ar sun rasa ransu inda ya bar mutane da yawa da munanan raunika.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel