Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Yadda uwa da yaranta su 3 suka mutu a lokaci guda

Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Yadda uwa da yaranta su 3 suka mutu a lokaci guda

- Wasu mutane hudu da suka hada da uwa da yayanta guda uku sun mutu sakamakon rushewar wani gini a yankin Magodo Phase I a Lagas a safiyar ranar Asabar

- Darakta janar na hukuma bayar da agajin gaggawa na jihar Lagas, Dr Olufemi Oke-Osanyitolu ya tabbatar da hakan

- Hakazalika mai gidan Emmanuel Utache ya ji manyan raunuka daban-daban

Labari dake zuwa mana ya nuna cewa wasu mutane hudu da suka hada da uwa da yayanta guda uku sun mutu sakamakon rushewar wani gini a yankin Magodo Phase I a Lagas a safiyar ranar Asabar.

Darakta janar na hukuma bayar da agajin gaggawa na jihar Lagas, Dr Olufemi Oke-Osanyitolu a tabbatar da hakan a wata hira da jaridar Daily Trust.

Lamarin ya afku ne a gida mai lamba 48 unguwa Orisha Water Front Otun Araromi, Magodo Phase I.

A cewar hukuma agajin, ginin ya ruguzo daga saman tsauni zuwa kan wani gini da ke kasa a unguwar inda yayi sanadiyar mutuwar uwa, kanwa da kuma yaranta guda biyu.

Sai dai, duk kokari da aka yi domin ceto su da ransu ya ci tura domin sun mutu yayinda mahaifinsu, Emmanuel Utache ya ji manyan raunuka daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun kama manyan kwamandojin Boko Haram 10 (kalli jerin sunayensu)

Wadanda suka mutu sun hada da Jumiah Utache (uwa); yar shekara tara Faith Emmanuel (kanwar matar); dan shekara biyu Domino Utache da kuma Daniel Utache.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel