Dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta dakatar da rubuta jarabawar malamai a jihar Ibadan

Dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta dakatar da rubuta jarabawar malamai a jihar Ibadan

- A yau ne a kalla malaman makaranta 69,000 a fadin kasar nan suka rubuta jarabawar neman shaidar zama kwararrun malamai

- Amma kuma sai gwamnatin tarayya ta dakatar da rubuta jarabawar a dakin rubuta jarabwar na jihar Ibadan

- Sakataren ma'aikatar ilimi ta kasa, Sonny Echonno yace, duk malamin da bai ci jarabawar ba bashi da muhalli a azuzuwan makarantun kasar nan

Gwamnatin tarayya ta dakatar da rubuta jarabawar malami a jihar Ibadan bayan da ta zargesu da rashin da’a.

Sonny Echono, babban sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayya, ya bayyana hakan ne a garin Abuja ga manema labarai jim kadan bayan da ya kammala tsare masu rubuta jarabawar.

Kamfanin dillanci labarai ya ruwaiti cewa, an kirkiro da jarabawar kwararrun malaman makarantar ne a 2017 kuma wadanda suka ci jarabawar kadai za a ba shaida zama kwararrun malaman makaranta.

KU KARANTA: Dalilin da yasa na wake shugaban kasa Muhammadu Buhari, in ji Alan waka

Ya jinjinawa hukumar malaman makaranta ta Najeriya da suka shirya jarabawar a cibiyoyi 47 na fadin kasar nan.

“A kalla malamai 69,000 ke rubuta jarabawar a fadin jihohi 36 na kasar nan har da birnin tarayya karkashin kular hukumar malaman makarantar ta Najeriya.”

“Rahoto daga jihar Ibadan ya nuna cewa akwai matsaloli, hakan kuwa yasa aka dakatar da rubuta jarabawar kuma muna kokarin ganin mun shawo kan matsalar. Akwai cigaba babba ta bangaren yadda aka tsara jarabawar. Akwai hoton mai rub uta jarabawar a gaban na’ura mai kwakwalwar da yake amfani da ita. Hakan kuwa zai hana satar jarabawa.” In ji shi.

Kamar yadda yace, an kirkiro jarabawar ne a tankade tare da rairaye malaman makarantar da basu dace da koyar da dalibai na. Duk kuwa wanda bai nasara a jarabawar ba, bas hi da muhalli a azuzuwan makarantunmu. Za a fara tabbatar da dokar ne na da watan Janairu na 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel