Bidiyo: Indai Smart ne ba tun yau na saba kada shi a zabe ba, inji Dino Melaye

Bidiyo: Indai Smart ne ba tun yau na saba kada shi a zabe ba, inji Dino Melaye

Sanata Dino Melaye ya ce da magoya bayansa su kwantar da hankalinsu game da zabensu da za a sake, shi da Smart Adeyemi na kujerar sanatan Kogi ta yamma.

Melaye ya fadi wannan maganar ne a lokacin da yake martani game da hukunci kotun daukaka kara wadda ta soke zaben ta kuma ba INEC umarni ta shirya wani sabon zaben.

KU KARANTA:Jastis Tanko: Alkalan Kotun koli ba su samun baccin awa 12 a rana

Kotun daukaka karar, a ranar Juma’a ta yanke hukuncin cewa a sake gudanar da wani sabon zabe, inda shi kuwa Dino Melaye yake fadin ya kayar da Smart har sau biyu a zabukan baya, don haka yanzun ma tarihine zai maimaita kansa.

A zaben da aka gudanar a watan Fabrairu, Dino Melaye na jam’iyyar PDP ne ya samu nasara inda ya tashi da kuri’a 85,395 yayin da Smart Adeyemi na APC ya zo na biyu da kuri’a 66, 901.

Jim kadan bayan kammala zaben ne Smart Adeyemi ya shigar da kara kotun zabe inda yake kalubalantar nasarar Melaye game da zaben.

Haka kuwa Smart ya samu nasara a kotun, inda alkali biyu cikin guda uku suka goyi bayan korafinsa yayin da daya ne kadai ya goyi bayan Dino, a don haka aka soke zaben Dino.

Har ila yau, wannan hukuncin bai wa Dino Melaye dadi ba inda ya garzaya zuwa kotun daukaka kara. A ranar Juma’a 11 ga watan Oktoba ne ita ma kotun ta sake tabbatar da hukuncin kotun zaben.

Dino Melaye ya wallafa wani faifan bidiyo a shafinsa na facebook inda yake cewa, shi wannan abin ko a jikinsa saboda ya san inda Smart ne ba yau ya fara kayar da shi a zabe ba. Kalli bidiyon a kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel