Sojoji sun kama manyan kwamandojin Boko Haram 10 (kalli jerin sunayensu)

Sojoji sun kama manyan kwamandojin Boko Haram 10 (kalli jerin sunayensu)

Rundunar sojin Najeriya tace ta kama manyan mambobin kungiyar yan Boko Haram 10 a Bitta da ke karamar hukumar Gwoza na Borno, yayinda suke kokariun tsere ma farautarsu da dakarun sojin ke yi.

Jagoran labarai na ayyukan rundunar sojin Najeriya, Kanal Aminu Iliyasu, ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya saki a ranar Asabar, 12 ga watan Oktoba a Abuja.

Ya bayyana cewa wani aiki mai cike da nasara da sojojin brigade 26 suka gudanar a ranar 9 ga watan Oktoba ne yayi sanadiya kamun masu laifin, kamfanin dillancin labaan Najeriya ta ruwaito.

A cewasa, da dama daga cikin wadanda aka kama sun yi aikin tuka motoci a lokacin mummuan harin Boko Haram a kan Gwoza a 2014.

KU KARANTA KUMA: Mafi karancin albashi: Gwamnatin tarayya ta ji tsoron yajin aiki, ta matso da ganawa baya da kungiyar kwadago

Iliyasu yace wadanda aka kama dukkansu daga karamar hukumar Bama da ke jihar Borno sun hada da:

1. Shettima Mustapha Umar

2. Abba Buji

3. Alhaji Bukar Madu-(KAHID – dan ta’addan Boko Haram da mukaminsa yake daidai da na Birgediya Janar)

4. Ali Hassan (Limamin yan ta’addan Boko Haram)

5. Alkali Laminu.

6. Bukur Mustapha

7. Buba Umaru (wanda aka sani da Uhuru) da kuma KAHID

8. Madu Nosobe

9. Mustapha Hussaine

10. Umar Jeddum.

Iliyasu ya bayyana cewa dakarun rundunar sojin Najeriya na gudanar da ayyuka a fadin kasar domin magance ayyukan ta'addanci, inda ya kara da cewa ayyuka da dama sun haifar da yaya masu idanu.

Ya kuma bayyana cewa dakarun soji a Kaduna, sun kama wasu da ake zargin barayin shanu ne sannan suka kwato shanaye 23 da aka sace a karamar hukumar Birnin Gwari.

A cewarsa, ana kokarin gano mammalakan shanayen da aka sace domin a mayar masu da kayansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel