Jastis Tanko: Alkalan Kotun koli ba su samun baccin awa 12 a rana

Jastis Tanko: Alkalan Kotun koli ba su samun baccin awa 12 a rana

Jastis Tanko Muhammad ya ce, akasarin alkalan kotun koli ta Najerya ba su samun baccin awa 12 a rana. Muhammad ya fadi wannan maganar ne ranar Juma’a 11 ga watan Oktoba a lokacin da yake karbar bakuncin kwamitin shari’a na majalisar dattawa a Abuja.

Alkalin alkalan ya ce, idan suka ce za su rika yin baccin awa 12 a ko wace rana kamar yadda malaman kiwon lafiya suke bada shawara, to kuwa shari’o’i da dama za su samu matsala.

KU KARANTA:Mafi karancin albashi: Gwamnatin tarayya ta ji tsoron yajin aiki, ta matso da ganawa baya da kungiyar kwadago

Tanko ya ce: “Ina tabbatar maku da cewa da yawa daga cikinmu bamu baccin awa 12 a ko wace rana. Ba kai tsaye muke rubuta hukunci ba, kawai da mun bushi iska sai mu ce kaza da kaza ya faru don haka anyi watsi ko kuma an tabbatar da abu kaza.

“Dole sai mun fitar da dalilai a kan sokewa, watsi ko kuma tabbatar da hukunci a kotun. Idan muna baccin awa 12 babu yadda za ayi mu iya rubuta wadannan abubuwa.”

Alkalin yayi korafi game da kudin da ake fitarwa ma’aikatar shari’a inda ya ce kudi yayi kadan. A cewarsa bukatun sashen shari’ar na da yawa kwarai da gaske.

“Idan kuka duba kudin da ake warewa sashen shari’a zaku ga cewa ko kusa da abinda ake bai wa ma’aikatar gwamnati guda daya bai kai ba.” Inji shi.

Michael Bamidele, shugaban kwamitin shari’a na majalisar dattawa ya ce, hakika bangaren shari’a na matukar kokari wurin tabbatar da adalci a kan lamuran kasar nan musamman a fannin siyasa.

Ya kuma kara da cewa, za suyi iya bakin kokarinsu ganin cewa an karawa sashen kudi, fiye da abinda ake basu a yanzu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel