Mafi karancin albashi: Gwamnatin tarayya ta ji tsoron yajin aiki, ta matso da ganawa baya da kungiyar kwadago

Mafi karancin albashi: Gwamnatin tarayya ta ji tsoron yajin aiki, ta matso da ganawa baya da kungiyar kwadago

Gwamnatin tarayya na tsoron wani abinda kan iya zama matsala ga tattalin arzikin Najeriya, a yinkurin da kungiyar ‘yan kwadago ke yin a tafiya yajin aikin kasa gaba daya daga ranar 16 ga watan Oktoba.

Jaridar Tribune online ta ruwaito cewa, a jiya Juma’a 11 ga watan oktoba, gwamnatin tarayya ta matso da ganawar da ta sanya a ranar Talata 15 ga watan Oktoba zuwa ranar Litinin 14 ga watan don gudun shiga yajin aikin.

KU KARANTA:Yanzu-yanzu: El-Rufai ya fadi kasafin kudin 2020 na Kaduna

Duk da haka kungiyar kwadago na nan a kan bakarta, saboda a daren ranar Juma’a ta sake fadin cewa maganar zuwa yajin aikin na daram dam.

A cigaba da shirin shiga wannan yajin aikin, kungiyar kwadago na sanar da dukkanin ‘yan kwadagon cewa maganar yajin aiki fa babu fashi ranar Laraba za su soma.

Tun daga ranar da maganar yajin aikin nan ta fito fili, hukumomin gwamnati wadanda suka shafi minister kwadago, Chris Ngige, majalisar dattawa da majalisar wakilai sun yita zama da kungiyar amma sai dai har yanzu a banza.

Abinda shugabannin kungiyar kwadagon ke korafi a kai shi ne, ya za ayi gwamnatin tarayya ta sanya ranar Talata a matsayin ranar da za ayi wannan zaman mai matukar muhimmanci duk da cewa sun san ranar Laraba kungiyar za ta shiga yajin aiki.

Jaridar Tribune ta sanar da mu cewa zaman kungiyar kwadagon da kwamitin kwadagon na majalisar dattawa bai tabuka wani abin a zo a gani ba, saboda maganar yajin aiki fa tana nan daram.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel