Tubabbun 'yan ta'adda sun sako kansila, matarsa, 'yarsa da wasu mutane biyu

Tubabbun 'yan ta'adda sun sako kansila, matarsa, 'yarsa da wasu mutane biyu

- Tubabbun 'yan ta'addan jihar Katsina sun sako wani kansila, matarsa, 'yarsa da wasu mutane biyu

- Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya nuna farincikinsa akan zaman lafiya da tsaron da ke kara tabbata a jihar

- Gwamnan yace, tubabbun 'yan ta'addan na cika alkawarinsu sannu akan hankali

Tubabbun 'yan ta'adda a jihar Katsina sun sako wani kansila, Alhaji Gambo Sama'ila Yarliyau, matarsa, 'yarsu mai shekara daya da kuma wasu mutane 2 da suka yi kwanaki 9 a hannunsu.

Takardar da babban daraktan yada labarai na gwamna Aminu Bello Masari ya sa hannu, Malam Labaran Malumfashi kumaya bawa manema labarai a jihar Katsina a ranar Asabar, ya ce an mika kansilan da iyalansa ga gwamnan a yammacin ranar juma'a.

KU KARANTA: Tirkashi: Gwamnatin jihar Zamfara zata sauke sarakuna 5 da dagatai 33 akan matsalar tsaro

Sauran mutanen biyu da aka saki an mikasu asibitin Kurfi saboda akwai alamar firgici a tare dasu.

Bayan karbar wadanda aka saka, Gwamna Masari ya bada kwarin guiwar cewa akwai lokacin da zai zo babu wanda yake hannun masu garkuwa da mutane. Gwamnan ya kara da cewa, masu garkuwa da mutanen suna cika alkawurransu a hankali.

Ya ce, "Jihar na more zaman lafiya da tsaro kuma muna nan zamu cigaba da tattaunawa da 'yan ta'addan wanda hakan na nufin ajiye makamansu".

Jaridar The Nation ta tunatar cewa, tattaunawa da 'yan ta'addan jihar Katsina da wasu jihohin yana kawo saukin ta'addanci a yankunan. Kwalliya na biyan kudin sabulu don kuwa ana ta samun zaman lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel