Yanzu-yanzu: El-Rufai ya fadi kasafin kudin 2020 na Kaduna

Yanzu-yanzu: El-Rufai ya fadi kasafin kudin 2020 na Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Asabar 12 ga watan Oktoba, 2019 ya gabatar da N254.4b a matsayin kasafin kudin jihar Kaduna na shekarar 2020.

Gwamnan wanda mataimakiyarsa, Hadiza Balarabe ta wakilta a wurin wani taron tattaunawa da jama’a game da kasafin kudin 2020, ya ce kudin ayyukan da aka soma na matsayin N62.9b.

KU KARANTA:Dino Melaye ya koma wasan kwaikwayon Nollywood bayan ya fadi a kotu

Gwamnan ya ce, kasafin idan aka kaddamar da shi zai bada damar kasara ayyukan da aka soma tare da yin sabbi a mazaunin kashi 72% da 28%.

El-Rufai ya ce: “Kasafin kudin 2020 abu ne wanda zai bamu damar cinma matsayar ayyuka daman a gwamnatinmu. Mun shirya kasafin kudin na shekara mai zuwa ya kasance N254.4bn, kudin manyan ayyuka za su kama N177.29bn.

“Kasafin kudin shekara mai zuwa shi ne mafi yawa a tarihin jihar Kaduna. Ba a taba samun gwamnatin da ta ware kasafin kudin da ya wuce yawansa ba. Akwai naira biliyan 62.9 na ayyukan da aka soma ba a kammala ba. Mafi yawancin manyan ayyukan kuwa sun ta’allaka ne a kan cigaban tattalin arziki da kudi naira bilyan 144.

“Ayyukan gina kasa kuwa domin kayata jihar Kaduna an ware masu kudi naira biliyan 68. Kamar dai yadda kuka sani muna cigaba da ayyukan fito da birnin Kaduna cikin sura mai kyau.

“Daga cikin ayyukan da za ayi da kudin akwai gina tituna sabbi guda 7 da kuma yin kwaskwarima ga wasu guda 14 a birnin Kaduna. Haka zalika akwai ire-iren wadannan ayyukan a biranen Kafanchan da Zaria.” Inji Gwamnan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel