Kasafin 2020: Aso Rock za ta kashe miliyan 18.5 kan abinci da sama da miliyan 45 kan fetur

Kasafin 2020: Aso Rock za ta kashe miliyan 18.5 kan abinci da sama da miliyan 45 kan fetur

Wani rabe-raben kasafin kudin 2020 ya nuna cewa fadar Shugaban kasar Najeriya za ta kashe N45,678,552 wajen siyan man fetur na janareton fadar Villa.

Takardar wanda jaridar Nigerian Tribune ta gani ya kuma nuna cewa masu girka abinci na fadar Villa a 2020 za su dafa wa yan babban gida da bakinsu abinci da iskar gas da ya kai kimanin naira miliyan 18.5.

Kayan makulashe da abinci zai ja N135,668,651, yayinda kunshin jin dadi zai ja N240,730,180.

An ware naira miliyan 91.6 domin siyan tayoyin motoci marasa jin harbi a fada Shugaban kasa.

Hakazalika za a kashe naira biliyan 4.451wajen gyara ginin fadar Shugaban kasa a 2020.

Gyare-gyaren mazaunin villar zai ci N69,693,262, yayinda gyare-gyaren gidaje zai ci N10,575,702.

KU KARANTA KUMA: 2023: Babu wani aibu idan arewa ta cigaba da mulki har nan da shekara 100 – Ango Abdullahi

Gaba daya Gwamnatin tarayya na da niyan kashe N58,446,014,724 a fadar Shugaban kasa a wannan shekarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel