Abunda Buhari ya fada ma Dino bayan gabatar da kasafin kudi a Abuja

Abunda Buhari ya fada ma Dino bayan gabatar da kasafin kudi a Abuja

Tun bayan bayyanar hoton shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yake nuna Sanata Dino Melaye da dan yatsarsa bayan ya gabatar da kasafin kudin 2020 a majalisar dokokin tarayya a ranar Talata, wanda har Dino yayi martani ta hanyar yi masa kirari, ya sa ana ta hasashe kan abunda Shugaban kasar ya fada ma sanatan.

Masu lura wadanda ke ta bibiyar tsamar dake tsakanin Melaye da gwamnatin Buhari da kuma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki sunyi hasashen cewa Buhari ya yi barazana ne ga sanatan. Amma wata majiya wacce ta kasance a wajen da abun ya faru ta bayyana cewa abunda Buhari ya fada ma Melaye ba barazana bane illa wani tambaya da ya kunshi abubuwa da dama.

A cewar majiyar, Buhari ya tambayi Melaye cewa: “Kana nufin har yanzu kana wannan zaure?”

Shakka babu, tambayar zai samu fassara daban-daban duba ya rigimar dake kewaye da Melaye.

KU KARANTA KUMA: 2023: Babu wani aibu idan arewa ta cigaba da mulki har nan da shekara 100 – Ango Abdullahi

Sanatan yayi sanyi sosai a majalisar dokoki na tara wanda aka alakanta hakan ga faduwar tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki a zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel