Yadda wani mutum da ya shiga ruwa ceto yaro dan shekara 11 suka mutu tare da yaron

Yadda wani mutum da ya shiga ruwa ceto yaro dan shekara 11 suka mutu tare da yaron

Ambaliyar ruwa tayi awon gaba da wani yaro mai shekara 11 mai suna Wasiu tare da wani da ya yi yunkurin ceto shi a Aboru da Iyana-Ipaja a jihar Legas a ranar Asabar.

Mutane biyun sun nutse cikin ruwan ne a wani babban magudanan ruwa da ya hada Aburo da Iyana-Ipaja kan Ige Road.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta ruwaito cewa mutane da dama sun taru a gaban wurin abinda ya faru duk fuskokinsu cike da bakin ciki.

An gano cewar iyayen yaran sun aike su sayo gas din girki ne a gidan mai amma suka fada cikin babban magudanan ruwan.

Mutane uku ne suka yi yunkurin ceto yaran inda suka yi nasarar ceto babban cikinsu amma daya daga cikin masu ceto da aka fi sani da suna Wasiu shima ya nutse a ruwan yayin da ya ke kokarin ceto karamin.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An gano man fetur a yankin arewa maso gabas - NNPC

A yayin da ya ke zantawa da NAN, Wani shugaban kungiyar cigaban al'umma a Oki, Mista Solomon Agboghoroma ya yi bakin cikin afkuwar lamarin inda ya ce gwamnati ta gaza gina gada a wurin domin kare afkuwar hakan.

Agboghoroma ya ce akwai bukatar a fadada magudanan ruwan da ke Aboru road tare da gina gada a Cement Bus Stop domin duk lokacin da akayi ruwan sama akan samu ambaliyar da ke jefa al'ummar wurin cikin hatsari.

Wani da abin ya faru a gabansa, Mista Suleiman Adedokun ya shaidawa NAN cewa wanda ya shiga ceto yaran mai suna 'Wasiu Stubborn' ya shiga magudanan domin ceto yaran amma ruwa ya tafi da su baki daya.

Adedokun ya ce, "Wasiu ya yi kokari ya yi kokarin kama yaran na biyu amma ya gaza fitowa daga cikin magudanan ruwan saboda karfin ruwan ya yi yawa.

"Rashin kyawun hanya na rashin fadin kwalbati ne ya janyo rasuwarsu domin yaran ba su san akwai magudanan ruwa ba a wurin shiyasa suka fada domin ruwa ya mamaye ko ina."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel