Kuna da yancin zama yan Shi’a amma ba yan IMN ba - IGP

Kuna da yancin zama yan Shi’a amma ba yan IMN ba - IGP

Inspekto Janar na yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, ya bayyana cewa mutane na da yancin kasancewa yan shi’a amma ba wai mambobin kungiya haramtaciyyar kungiya ta proscribed Islamic Movement in Nigeria (IMN) ba.

Shugaban yan sandan yayi furucin ne a wata hira da jaridar Daily Trust a Ingila inda ya kasance wani mamba na tawaga gwamnatin tarayya da suka gana da kwararru a fannin doka da kuma ziyartan wasu kafofin watsa labaai na kasa da kasa a Landan kan shari’ar $9.6bn tare da Process and Industrial Development (P&ID).

Legit.ng ta tattaro cewa Adamu yace lallai kungiya IMN ta yan ta’adda ne sannan kuma cewa za a yi musu riko na yan ta’adda.

Ya kuma yi Karin haske kan cewa ba dukkanin yan Shi’a ake hari ba; kawai wadanda suka bayyana kansu a matsayin mambobin kungiyar IMN ne ake hari.

KU KARANTA KUMA: 2023: Babu wani aibu idan arewa ta cigaba da mulki har nan da shekara 100 – Ango Abdullahi

Yace: “A’a, ba yan Shi’a ake hari ba. Akwai wata kungiya da ake kira Islamic Movement in Nigeria. An haramta wannan kungiya.

“Don haka idan kai mamba ne, toh dan ta’adda ne kai; idan kana ganin ka fita daga wannan kungiya, sai kayi da’a sannan ka san da gwamnati, saboda su basu san kundin tsarin mulki ba, basu mutunta doka."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel