Zamfara: Sojoji sun kashe 'yan bindiga 100 yayin da suka yi yunkurin kai hari gonar tsohon gwamnan jihar

Zamfara: Sojoji sun kashe 'yan bindiga 100 yayin da suka yi yunkurin kai hari gonar tsohon gwamnan jihar

Dakarun sojojin Najeriya a ranar Alhamis a Zamfara sun dakile wata hari inda suka kashe wasu 'yan bindiga da suka yi yunkurin yin kutse cikin gonar tsohon gwamnan jihar, Ahmad Yarima.

Mazauna garin sun ce 'yan bindiga kimanin 200 suka kai harin gonar da ke karamar hukumar Bakura inda suka kashe masu gadi biyu da ke kula da gidan gonar.

Wata majiya ta ce sojoji biyar ne suka mutu yayin artabun duk da cewa Premium Times ba ta tabbatar da wannan ikirarin ba.

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta saboda dalilan tsaro ta ce, "Mun sanar da sojoji harin, sun iso kuma suka yi musayar wuta da 'yan bindigan inda 'yan bindiga fiye da 100 suka mutu."

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An gano man fetur a arewacin Najeriya - NNPC

Majiyar ta kuma ce, "An kama daya daga cikin 'yan bindigan da kudi fiye da N400,000 a tare da shi."

Ya kuma ce, "sojoji biyar sun mutu yayin da wasu hudu suka jikkata."

"Na kidaya gawarwakin sojojin a cikin mota kirar Hilux. Daga bisani an kai gawarwakin Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Gusau," inji majiyar.

Mai magana da yawun rundunar sojoji na Operation Hadarin Daji a Zamfara, Oni Orisan ya tabbatar da afkuwar harin.

Ya ce sojojin sun "farwa 'yan bindigan bayan harin da suka kai a Bakura. Ina aiki a kan rahoton a halin yanzu. Zan tuntube ku nan ba da dadewa ba."

Zamfara na daya daga cikin jihohin da ake fama da rashin tsaro na harin 'yan bindiga da garkuwa da mutane.

Gwamnatin jihar ta fara tattaunawa da 'yan bindigan domin ganin yadda za a kawo karshen hare-haren.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel