Wani marubuci ya yi karar El-Rufai da IG na 'yan sanda a kotu, ya nemi a biya shi N500m

Wani marubuci ya yi karar El-Rufai da IG na 'yan sanda a kotu, ya nemi a biya shi N500m

Wani mai wallafa labarai kuma rajin kare hakkin bil adama, Stevenm Kefas da ke tsare a gidan gyaran hali a Kaduna ya shigar da gwamnan jihar, Nasir El-Rufai da Sufeta Janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu da wasu mutum hudu kara a kotu kan zargin keta masa hakkinsa na 'dan adam.

The Punch ta ruwaito cewa Kefas ya bukaci wadanda ya yi karar su biya shi naira miliyan 500.

A ranar Juma'a, Kefas ya shafe kwanaki 144 a gidan gyaran hali ba tare da beli ba kan zarginsa da yin wasu kalamai na batanci kan El-Rufai.

Sai dai a ranar Alhamis, dan gwagwarmayar ya shigar da kara a babban kotun tarayya na jihar Kaduna ta hannun lauyansa, Gloria Ballason.

A karar da ya shigar, Kefas ya lissafa wadanda suka keta masa hakkinsa na dan adam kamar haka:

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An gano man fetur a yankin arewa maso gabas - NNPC

1. Cafra Caina, Shugaban karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna

2. Aisha Dikko, Mai bawa gwamnan Kaduna shawara kan shari'a

3. Gwamna Nasir El-Rufai

4. Alkalin alkalan jihar Kaduna

5. Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kaduna

6. Sufeta Janar na 'yan sanda

A karar da ya shigar a ranar 10 ga watan Oktoban 2019 mai lamba FHC/KD/62/19, Kefas ya bukaci kotu bi masa hakkokinsa ta ya ce an take da suka hada da kama shi ba tare da kwakwaran dalili ba, bata masa suna, cin zarafinsa da sauransu wanda sun saba wa wasu sassan na kudin tsarin mulkin Najeriya da ma wasu dokokin kare hakkin bil adama na duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel