2023: Babu wani aibu idan arewa ta cigaba da mulki har nan da shekara 100 – Ango Abdullahi

2023: Babu wani aibu idan arewa ta cigaba da mulki har nan da shekara 100 – Ango Abdullahi

Shugaban kungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana cewa yankin arrewa na iya cigaba da rike mulkin kasar har nan da shekaru 100 idan tana so, cewa damokradiyya na kunshe da adadi ne da kuma yankin dake da karfin cimma hakan.

Abdullahi ya bayyana hakan yayinda yake magana akan sanin rabe-raben wa’adin shugabanci yayinda Najeriya ke duba ga sabon zaben kasar a 2023.

Ya fada ma jaridar Daily Sun cewa arewa za ta marawa yan takara daga yankin ne kawai baya a tseren shugabancin kasa na 2023.

Ya mayar da hankali ga cewa rabe-raben shugabanci zuwa yanki-yanki, wanda mafi akasarin shugabannin kudu ke fafutuka akai ya saba ma kundin tsarin mulki sannan kuma cewa shugabannin arewa ba za su goyi bayan haka ba.

Ya kara da cewa yan arewa za su marawa duk jam’iyyar da ta gabatar da dan takara daga arewa baya a 2023.

KU KARANTA KUMA: Sarki Sanusi ya yabawa Ganduje a kan shirin bayar da ilimi kyauta a Kano

Wata yarinya 'yar shekara biyar a duniya ta zama gwamnar jihar Zamfara ta rikon kwarya ta tsawon minti biyu.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya mika ragamar mulkin jihar Zamfaran na tsawon mintuna biyu ga wata karamar yarinya 'yar asalin karamar hukumar Tsafe dake jihar ta Zamfara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel