Alexei Leonov: Mutum na farko da ya fara 'tafiya' a sararin samaniya ya rasu

Alexei Leonov: Mutum na farko da ya fara 'tafiya' a sararin samaniya ya rasu

Hukumar Nazarin Sararin Samaniya na kasar Rasha ta sanar da rasuwar Alexei Leonov, mutum na farko a duniya da ya fara 'tafiya' a sararin samaniya shekaru 54 da suka gabata wadda ya rasu a birnin Moscow yana da shekaru 85 a duniya.

A sanarwar ta ta fitar a shafin ta na Intanet, Roscosmos ta ce Leonov ya rasu ne a ranar Juma'a 11 ga watan Oktoban 2019. Leonov ya yi 'tafiyarsa' ta farko a sararin samaniya a ranar 18 ga watan Maris na 1965 yayin da ya fita daga Vokshod 2 tare da taimakon wani abin da ake kira tether.

A tafiyarsa zuwa sararin samaniya karo na biyu shekaru 10 bayan zuwan farko, Leonov ya jagoranci rabin tawagar Apollo-Soyuz 19 mission. Wannan shine karo na farko da masu nazarin sararin samaniya na Rasha suka yi hadin gwiwa da na Amurka.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An gano man fetur a jihar Bauchi - NNPC

Mista Leonov ya cika shekaru 85 a duniya watan Mayu.

A cikin 'yan kwanakin nan, wasu masu nazarin sararin samaniya na kasa da kasa sun tafi sararin samaniya inda suka lika hotunansa a jikin jirginsu suna taya shi murnar zagoyowar ranar haihuwarsa daga sararin samaniya.

Za ayi jana'zar Leonov a ranar Talata a makabartar tunawa da sojoji da ke wajen birnin Moscow.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel