Tirkashi: Gwamnatin jihar Zamfara zata sauke sarakuna 5 da dagatai 33 akan matsalar tsaro

Tirkashi: Gwamnatin jihar Zamfara zata sauke sarakuna 5 da dagatai 33 akan matsalar tsaro

- Kwamitin binciken tsaro na jihar Zamfara ya ba gwamnatin jihar shawarar sauke sarakuna 5, dagatai 33 da wasu masu anguwanni

- Kwamitin binciken ya zakulo wasu sojoji 10 da wasu 'yan sanda da ke da sa hannu a tabarbarewar tsaro a jihar

- Gwamnan jihar ya ce rantsuwar da yayi don kare hakkokin mutane duk da banbancin siyasa, kabila da addini bazata tashi a banza ba

Kwamitin da gwamnatin jihar Zamfara ta kafa don shawo kan matsalar tsaron jihar ta bada shawarar sauke sarakuna 5 da dagatai 33 a rahoton da suka mika ranar juma'a.

Yayin mika rahoton ga gwamna Muhammad Bello Matawalle, shugaban kwamitin, Alhaji M.D Abubakar, tsohon sifetan 'yan sanda mai murabus, ya ce sarakunan 5, dagatai 33 da wasu masu anguwanni a jihar na da sa hannu a tabarbarewar tsaron jihar.

KU KARANTA: Lawan ya bawa ministoci wa'adin kare kasafin kudin ma'aikatunsu

Tsohon sifetan 'yan sandan ya ce, "Kwamitin na bada shawarar sauke sarakuna 5, dagatai 33 da kuma masu anguwannin da ke da sa hannu a matsalar tsaron."

Kamar yadda kwamitin ya sanar, daga rahoton da suka samu, za a gurfanar da daya daga cikin sarakunan a kotu saboda zarginsa da ake da taimakawa kashe-kashe da boye 'yan ta'addan.

Kwamitin ya kuma bada shawarar gyara ga yanayin mulkin duk masarautu 17 da ke jihar don tsaftace yanayin sarautar gargajiyar jihar.

Kwamitin ya kara da bawa gwamnatin tarayya shawarar gurfanar da sojoji goma a kotun sojin Najeriya akan hannunsu tsundum da ta kama a mummunan aikin a jihar.

Kwamitin ta kara da shawartar hukumar 'yan sanda da ta kori jami'anta 4, wasu hudun kuma ta rage musu matsayi sai kuma 7 ta kara musu girma.

Shugaban kwamitin ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da shawarwarin kwamitin don kuwa zaman lafiyar jihar ya dogara ne a kokarin gwamnan na cire banbancin siyasa yayin zartar da hukunci.

A maida martaninsa, gwamna matawalle ya jinjinawa kwamitin akan aikin da suka yi. Ya kuma tabbatar musu da cewa, rantsuwarsa ta kare hakkoki da rayuwar mutanen jihar duk da banbancin siyasa, kabila ko addini bazata tashi a banza ba.

Ya kara da cewa, zai gana da shugaban kasa akan shawarwarin da suka danganci gwamnatin tarayya.

Duk da kuwa kwamitin bai sanar da sarakunan da abun ya shafa ba yayin mika rahoton, wasu daga cikin sarakunan basa wajen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel