Gwaggon biri ya addabi mutanen wani kauye a kasar Afrika ta Kudu yayin da yake bin 'yan luwadi yana yi musu fyade

Gwaggon biri ya addabi mutanen wani kauye a kasar Afrika ta Kudu yayin da yake bin 'yan luwadi yana yi musu fyade

- Wani fitanannen gwaggon biri ya addabi mutanen wani kauye a kasar Afrika ta Kudu

- Birin ya kware wajen tare maza yayi musu fyade a kauyen, kuma abin mamaki shine iya maza kawai yake bi

- An bayyana cewa birin yana yawo shi daya ne kawai, ya bar cikin ayarin 'yan uwansa ya dawo yiwa mutane fyade

Maza a yankin arewa maso yammacin kasar Afrika ta Kudu suna zaune cikin fargaba bayan wani katon gwaggon biri da yake son saduwa da maza a yankin ya addabe su.

An bayyana cewa birin ya kai wa kimanin mutane shida hari, inda duk kuma ya sadu da su, kuma abin mamakin shine birin iya 'yan luwadi kawai yake bi, ba ruwan shi da kowa, kuma suma 'yan luwadin baya cutar da su, sai dai kawai yayi lalata da su ya wuce abin sa.

Wani wanda abin ya rutsa da shi mai suna George Chiune ya ce yana tsakar tafiyar sa kawai sai ji yayi birin ya danne shi. "Na yi tunanin kashe ni zai yi, amma daga baya na gane cewa ga abinda ya kawo shi," in ji George.

Yanzu haka dai an kwantar da mutane biyar a asibiti inda suke fama da ciwo a duburar su. Likitocin sun bayyana cewa mutanen sun kamu da ciwon daji na dubura.

KU KARANTA: Hotuna: 'Yar shekara biyar ta zama gwamnan rikon kwarya ta minti biyu a jihar Zamfara

Birin wanda aka sanyawa sunan banza da Somizi yana tafiya shi daya ne ba tare da 'yan uwansa ba, kuma a cewar wani masani a bangaren dabbobi wannan wani sabon al'amari ne da ba su saba gani ba, inda ya ce su irin wannan biran an san su da tafiya a cikin tawaga tare da 'yan uwansa.

Wata masaniya a bangaren mai suna Lizzie McKenzie ta bayyana cewa: "Akwai yiwuwar birin ya addabi 'yan uwansa ne shine suka kore shi daga cikin su, shine dalilin da ya sanya yake yawo shi daya, amma kuma dalilin da ya sanya yake bin maza abin yana bani mamaki. Ban taba ganin irin wannan lamarin a wajen biri, kuma na karance su na tsawon shekara 20," in ji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel