Sarki Sanusi ya yabawa Ganduje a kan shirin bayar da ilimi kyauta a Kano

Sarki Sanusi ya yabawa Ganduje a kan shirin bayar da ilimi kyauta a Kano

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yabawa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano saboda bullo da shirin ilimin frimare zuwa sakandare na kyauta a jihar duk da sa-in-sa da ke tsakaninsu.

Sanarwar ta mai magana da yawun gwamnan, Abba Anwar ya fitar a ranar Juma'a ya ce Sarkin ya yabawa gwamnan kan shirin inda ya ce, "Nayi imanin cewa an kaddamar da wannan shirin ne domin yi wa kanawa da al'umma hidima."

Sanarwar ta ce an jiyo Sanusi na cewa, "Wannan shine irin abinda kasar nan ke bukata. Ya kamata mu mayar da hankali kan cimma wannan shirin domin ilimi shine turbar cigaban kowane al'umma.

"Abinda gwamnan keyi abin koyi ne kuma anyi ne domin cigaban al'umman mu kuma ina fatan wasu jihohin su za yi koyi da irin sallon mulki na mai girma gwamna."

DUBA WANNAN: Tausayi: Bidiyon yadda Sarki Sanusi ya zubar da hawaye yayin bayar da labarin wata mata a Kano

Sanarwar ta kuma ce ya kamata gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki su hada kai wuri guda su tabbatar cewa al'ummarsu sun zama abin alfahari ba dauyi a gare su ba.

Ya ce, "Kamar yadda gwamnan ya nuna ya kamata yawan al'ummar mu ya zama alheri a gare mu ba nauyi ba."

Sarkin ya shawarci dukkan jihohin Najeriya su rungumi shirin da ya ce 'babban hanya ce ta yi wa al'umma hidima."

Mista Anwar ya ce sarkin ya yi wannan yabon ne lokacin da gwamnan ya ke ganawa da wata tawaga daga Zenith Bank karkashin jagorancin shugaban yankin Arewa maso Yamma, Sani Yahaya a gidan gwamnati kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel