Kotun zabe ta tabbatar da nasarar Gwamna Fintiri na jam'iyyar PDP

Kotun zabe ta tabbatar da nasarar Gwamna Fintiri na jam'iyyar PDP

Kotun sauraron karrarkin zaben gwamna da ke zamanta a Yola ta yi fatali da karar da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta shigar na neman a soke zaben gwamnan jihar Adamawa.

Bayan nasarar da dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Ahmadu Fintiri ya yi kan gwamna Muhammadu JIbrilla Bindow, jam'iyyar APC ta shigar da PDP, Fintiri da INEC kara a kotu.

Mai shari'a Adediran Adebara ya yi watsi da karar da aka shigar kan wasu dalilai biyu inda ya jadada nasarar da Gwamna Fintiri ya yi a babban zaben na 2019.

DUBA WANNAN: Tausayi: Bidiyon yadda Sarki Sanusi ya zubar da hawaye yayin bayar da labarin wata mata a Kano

A yayin da ya ke yanke hukuncin a ranar Juma'a, Adebara ya ce wanda ya shigar da karar ya gaza gabatar da hujjoji da ke tabbatar da zargin da su kayi na yin zabe ba bisa ka'ida ba da rashin bin dokokin zabe yayin kada kuri'u.

Lauya da ke kare wanda ya shigar da kara, Barrister Ibrahim Effiong ya ce tawagarsu za suyi nazarin hukuncin da kotun ta bayar sannan su bawa wanda suke karewa shawarar abinda ya dace ya yi.

A yayin da ya ke tsokaci kan hukuncin, Shugaban ma'aikata na fadan Fintiri, Farfesa Maxwell Gidado ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga demokradiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel