Wadanda suka yi garkuwa da Shugaban makaranta a Kaduna sun nemi a biya N20m kudin fansa

Wadanda suka yi garkuwa da Shugaban makaranta a Kaduna sun nemi a biya N20m kudin fansa

Yan bindigan da suka yi garkuwa da Shugaban makarantar sakandare na Government Technical College, Mararaban Kajuru, da ke karama hukumar Kajuru, a jihar Kaduna, Mista Francis Maji, sun bukaci a biya kudin fansa naira miliyan 20.

Wata majiya ta kusa da makaranta ta bayyana wa jaridar Punch a wayar tarho cewa masu garkuwan sun tuntubi iyalinsa ta dayan wayan Shugaban makarantan inda suka gabatar da bukatarsu.

Wasu yan bindiga a tsakar daren ranar Alhamis, ne suka kai mamaya makarantar sannan suka yi garkuwa da Shugaban makarantar.

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin.

Garkuwan na zuwa ne mako guda bayan yan bindiga sun sace dalibai mata shida, da ma’aikata biyu a kwalejin Engravers College, Kakau Daji a karamar hukumar Vhikun da ke jihar.

Wani malamin makarantar day a nemi a sakaya sunansa yace yan bindigan da yawansu ya kai sama da 20 sun farma makarantar da misalign karfe 12:00 na dare sannan suka fara harbi a sama inda suka tafi da Shugaban makarantar daga gidansa.

KU KAANTA KUMA: Yan bindiga sun karbi N3bn a matsayin kudin fansa a Zamfara - Kwamiti

Majiyar tace daga iyalansa har hukumar makarantar basu da hanyar biyan kudin fansar domin ceto Shugaban nasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel