Dino Melaye ya koma wasan kwaikwayon Nollywood bayan ya fadi a kotu

Dino Melaye ya koma wasan kwaikwayon Nollywood bayan ya fadi a kotu

Sanata Dino Melaye na jihar Kogi a ranar Juma’a yayi magana game da hukuncin da kotun daukaka kara ta jaddada inda ta tabbatar da hukuncin soke zabensa da lashe a baya.

Yayi maganar ne jim kadan bayan kotun daukaka karar ta tabbatar da rashin nasararsa inda ta ce za a sake zaben kujerar sanata mai wakiltar Kogi ta yamma.

KU KARANTA:Zamu yi duk abinda ya kamata domin kulla kyakkyawar alaka da Majalisa, inji Buhari

A daidai wannan lokacin ne aka hangi Sanatan tare da wasu ‘yan wasan kwaikwayon turanci na Nollywood, Cif Dan Nwayanwu, Linc Edochie, Victor Decke, Cif Bruno Iwuola da kuma Paul Sambo.

Da yake magana a kan dalilinsa na shiga cikin shirin wasan kwaikwayon Dino Melaye ya ce: “Na shiga wannan shirin ne domin janyo hankalin al’umma a kan rashin gaskiya.” Da kuma yake magana game da hukuncin kotun, sanatan ya ce babu damuwa a tare da shi ko kadan,

“Ina matukar farin cikin fitowa a cikin wannan shirin wasan kwaikwayo kasancewar matsalar al’ummarmu ce muke magana a kai cikinsa.

“Ni ba sabon shiga shirin wasannin kwaikwayo bane saboda ko lokacin da nayi bautar kasa na NYSC na lashe lambar yabo a fagen wasan kwaikwayo.

“A shirye nake da in yiwa Najeriya aiki a duk inda ta kama, don haka idan wata dama mai kama da wannan ta sake zo mani zan karbeta hannu biyu-biyu.” Inji Dino.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel