Yan bindiga sun karbi N3bn a matsayin kudin fansa a Zamfara - Kwamiti

Yan bindiga sun karbi N3bn a matsayin kudin fansa a Zamfara - Kwamiti

Kwamitin da Gwamna Bello Matawalle ya kafa domin nemo mafita akan lamarin fashi da makami a Zamfara, ya bayyana cewa yan bindiga sun karbi naira biliyan 3 a matsayin kudin fansa daga yan uwan mutanen da suka yi garkuwa dasu a jihar.

Shugaban kwamitin, Mohammed Abubakar, tsohon sufeto janar na yan sanda, ya bayyana hakan yayin gabatarwa da gwamnan rahoton kwamitin a ranar Juma’a, 11 ga watan Oktoba a Gusau.

Ya bayyana cewa rahoton na kunshe ne da abunda ya faru daga watan Yunin 2011 zuwa 29 ga watan Mayun 2019.

Yace an karbi kudaden ne daga yan uwan mutane 3,672 wadanda suka biya kudin domin ceto yan uwan nasu.

Abubakar ya bayyana cewa mata 4,983 aka mayar zawarawa, an mayar da yara 25,050 maayu sannan aka mayar da mutane 190,340 marasa galihu duk a sanadiyar hare-haren yan bindiga na wannan lokacin.

Ya kuma bayyana cewa Fulani makiyaya da basu ji ba basu gani ba sun rasa shanaye 2,015, akuyoyi da tunkiyoyi 141, rakuma da jakuna 2,600 ga barashin shanu yayinda aka kona ababen hawa 147,800 a wurare daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Babu wanda ya rufe Aisha Buhari a fadar Shugaban kasa, bidiyon dake yawo duk karya ne

Tsohon Shugaban yan sandan yace, domin cimma zaman lafiya mai dorewa, ya zama dole gwamnatin jihar ta karbe dukkanin gonaki da ke a hanya sannan ta fara bin tsarin kiwo na zamani ta yadda makiyaya za su kasance a wuri daya.

Da yake karban rahoton, Gwamna Matawalle yayi alkawarin aiki da shawarwarin, sannan ya bayar da tabbacin cewa ba zai bari son zuciya ya dauke hankalinsa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel