Kasafin kudi: Buhari ya hana ministoci tafiya kashashen ketare

Kasafin kudi: Buhari ya hana ministoci tafiya kashashen ketare

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci dukkan ministocinsa da shugabanin hukumomin gwamnati su soke duk wata tafiya da za suyi zuwa kasashen ketare har sai zuwa lokacin da aka kammala kare kasafin kudin 2020 a majalisar tarayya.

Direktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Wille Bassey ne ya bayar da wannan sanarwar a ranar Juma'a.

Sanawar ta ce, "Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin dakatar da duk wani tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da ministocinsa ko shugabanin hukumomi za suyi domin bawa ministocin damar jagorancin kare kasafin kudin da ke gaban majalisar dattawa."

DUBA WANNAN: Tausayi: Bidiyon yadda Sarki Sanusi ya zubar da hawaye yayin bayar da labarin wata mata a Kano

"Dakatar da tafiye-tafiyen zai bawa hukumomi da ma'aikatun gwamnati daman bawa sashin masu zartarwa hadin kai da ya kamata domin tabbatar da cewa an amince da kasafin kudin a kan lokaci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel