An kama wadanda ake zargi sun kashe sojoji 5 a Plateau

An kama wadanda ake zargi sun kashe sojoji 5 a Plateau

Dakarun sojoji na Operation Safe Haven (OPSH) da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a wasu sassan jihohin Plateau da Bauchi ta yi ikirarin cewa ta kama wadanda suka kashe wasu sojoji biyar wadanda ke aiki ta rundunar.

Kwamandan OPSH, Austine Agundu ya shaidawa manema labarai a hedkwatan rundunar a ranar Alhamis cewa an kama wadanda ake zargi da kisar a kauyen Bet da ke karamar hukumar Barikin Ladi na jihar Plateau.

Mista Agundi ya yi ikirarin cewa wadanda ake zargin sun amsa cewa sun da hannu cikin kisar sojoji uku a ranar 6 ga watan Satumba da wasu sojojin biyu a ranar 28 ga watan Satumba.

DUBA WANNAN: Tausayi: Bidiyon yadda Sarki Sanusi ya zubar da hawaye yayin bayar da labarin wata mata a Kano

"A wan sumame da aka kai, sojojin sun kama mutum 6 da ake zargin 'yan bindiga ne. Sun bayyana cewa suna da hannu cikin harin da aka kai kan sojoji a kauyen Nding Sesut a karamar hukumar Barikin Ladi wadda ya yi sanadiyar rasuwar sojojin operation safe haven uku a ranar 6 ga watan Satumba.

"Binciken da aka gudanar kawo yanzu ya nuna cewa suna da hannu ciki harin da aka kaiwa sojoji a Fan District a karamar hukumar Barikin Ladi da Kwanan Fulani a karamar hukumar Riyom da ya yi sanadin mutuwar sojojin operation safe haven 2 a ranar 28 ga watan Satumban 2019."

"Binciken ya nuna cewa 'yan bindigan suna da alaka da wasu 'yan bindigan a yankin Arewa maso Tsakiya na kasar," inji Agundi.

Janar Agundi ya gargadi masu daukan nauyin wadanda ke aikata laifukan nan su tuba su dena kuma ya yi kira ga al'umma su rika baya rundunar bayyanai masu amfani da zai taimaka wurin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel