INEC ta sa ranar sake sabon zaben su Sanata Dino Melaye

INEC ta sa ranar sake sabon zaben su Sanata Dino Melaye

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta ce tana duban amfani da ranar 16 ga watan Nuwamba don sake zaben su Sanata Dino Melaye

- Ganin cewa kwanaki 34 suka rage a yi zaben gwamnan jihar, hukumar tace akwai yuwuwar hada zabukan rana daya

- Kwamishinan zaben yankin ya ja kunnen manema labarai akan su guji labaran bogi da illolin da zasu iya haifarwa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta ce tana duban yuwuwar sake zaben sanatan jihar Kogi ta yamma a ranar 16 ga watan Nuwamba da za a yi zaben gwamnan jihar.

Kwamishinan zabe mai kula da jihohin Kogi, Nasarawa da Kwara, Alhaji Mohammed Haruna ya bayyana hakan a ranar juma'a a garin Lokoja.

Yayin amsa tambayoyin manema labarai bayan kammala zaman kotun da ya soke nasarar sanata Dino Melaye, Haruna ya ce tunda akwai kwanaki 34 da suka saura na zaben gwamnan, akwai yuwuwar a hada da na sanatan.

KU KARANTA: Majalisar jihar Zamfara ta haramtawa 'yan majalisa tattauna matsalar tsaro a zauren majalisa

A yau ne kamfanin dillancin labarai ta ruwaito cewa, kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben sanata Melaye na jam'iyyar PDP kuma ta umarci INEC da ta yi sabon zabe a yankin cikin kwanaki 90 da yanke hukuncin.

Hukuncin ya biyo bayan karar da Sanata Smart Adeyemi na jam'iyyar APC ya mika ga kotu a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Kwamishinan INEC din ya sauka garin Lokoja akan taron gogarwar da aka yi wa manema labarai akan labaran bogi da gidauniyar zabe ta duniya (IFES) ta shirya tare da hadin guiwar INEC.

Haruna ya sanar da wadanda aka horar din da su guji labaran karya da kuma abubuwan da zasu iya jawowa.

Ya kara da jawo hankalinsu da su goyi bayan hukumar zaben mai zaman kanta ta don tabbatar da zabe mai inganci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel