Babu wanda ya rufe Aisha Buhari a fadar Shugaban kasa, bidiyon dake yawo duk karya ne

Babu wanda ya rufe Aisha Buhari a fadar Shugaban kasa, bidiyon dake yawo duk karya ne

Rahotanni sun bankado cewa wani bidiyo dake ta yawo inda aka nuno uwargidar Shugaban kasa Aisha Buhari cikin fushi kan zargin rufeta a wani bangare na fadar Shugaban kasa bayan ta dawo kasar a ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoba ba gaskiya bane, na bogi ne.

Jaridar TheCable a ruwaito cewa a yanzu haka uwargidar Shugaban kasar bata dawo daga kasar Ingila ba.

Tun a ranar Laraba ne ake ta yada jita-jitan cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai auri mata ta biyu. Anyi zargin cewa Shugaban kasar zai raya sunnah ne da Sadiya Umar Farouq, ministar kula da harkokin agaji da kare yaduwar annoba, a ranar Juma’a, 11 ga watan Oktoba.

Anyi ta yada jita-jitan cewa uwargidar Shugaban kasar ta dawo kasar domin nuna fushinta akan lamarin, amma sai na kewaye da Aso Rock suka rufe ta.

KU KARANTA KUMA: Bankada: Wani shafi dake yiwa Sadiya Farouq sojan gona yayi martani kan rade-radin auranta da Buhari

Sai dai hasashen ya zama karya domin uwargidar Shugaban kasar na chan a kasar Ingila har yanzu, yayinda Sadiya Farouq ke a birnin New York a yanzu haka, inda take yada kamfen din majalisar dinkin duniya na yaki da talauci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel