Zamu yi duk abinda ya kamata domin kulla kyakkyawar alaka da Majalisa, inji Buhari

Zamu yi duk abinda ya kamata domin kulla kyakkyawar alaka da Majalisa, inji Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari yayi alkawarin yin duk wani abu da ya dace domin karfafa kyakkyawar alaka tsakanin bangaren Zartarwa da Majalisar dokokin Najeriya.

Buhari ya fadi wannan maganar ne ranar Juma’a 11 ga watan Oktoba, 2019 a wurin taron kaddamar da kudurin majalisar wakilai ta 9 a Abuja.

KU KARANTA:Dino Melaye:Yahaya Bello ya taya Adeyemi murnar samun nasara a kotun daukaka kara

Shugaban kasan wanda ya samu wakilcin Ministan muhalli, Dr Mohammed Abubakar, ya ce a shirye yake da yin duk abinda ya kamata domin kulla kyakkyawar alaka da majalisar saboda cigaban ‘yan Najeriya.

Buhari ya ce wannan magana ce mai matukar amfani wadda idan aka soma aiki da ita za ta kawowa kasar cigaba gaba dayanta.

Ya kuma yi kira ga ‘yan majalisan da su rinka kawo kudurin da zai tsare martabar ‘yan Najeriya ya kuma habbaka tattalin arziki tare da gyara alakar kasa da kasa.

Shugaban kasan ya kara da cewa dukkanin ma’aikatu da kuma hukumomin gwamnatin Najeriya za su bayyana gaban majalisar domin amsa tambayoyi a kan kasafin kudin 2020.

A na shi jawabin kuwa, Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya ce suna bukatar ganin kasafin kudi mai cike da shiri na musamman ga matasa da kuma tattalin arziki domin kare martabar Najeriya.

Ya kuma kara da cewa, duk abinda sashen zartarwa ya yanke domin ‘yan Najeriya, majalisarsu a shirye take domin rattaba hannu tare da amincewa da kudurin saboda cigaba ‘yan kasa.

Game da amsar tambayoyin kasafin kudin 2020 wanda hukumomin gwamnatin za suyi, Lawan ya ce idan har akwai jami’in da ke son yin tafiya kasar waje, to yazo ayi masa na shi tambayoyin kafin watan Oktoba ya kare.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel