Lawan ya bawa ministoci wa'adin kare kasafin kudin ma'aikatunsu

Lawan ya bawa ministoci wa'adin kare kasafin kudin ma'aikatunsu

- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana hukuncin da majalisar zata yi wa ministoci ko shuwagabannin ma'aikatun tarayya da suka ki zuwa kare kasafin kudin su na shekara

- Ya bayyana cewa, zasu ba da daga nan zuwa karshen watan Oktoba don ministocin su samu damar yin hakan

- Majalisar ta tabbatar da cewa, tana son aminta da kasafin kudin 2020 ne kafin karewar wannan shekarar

A ranar juma'a ne shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya ja kunnen ministoci da shuwagabannin cibiyoyin gwamnati akan cewa matukar basu kare kasafin kudinsu na shekara ba kafin karshen watan Oktoba, toh bazasu samu damar yin hakan ba.

Lawan ya ce, majalisar dattawan bazata aminta da duk wani yunkurin hana su aminta da kasafin kudin 2020 kafin karewar shekarar nan.

KU KARANTA: Majalisar jihar Zamfara ta haramtawa 'yan majalisa tattauna matsalar tsaro a zauren majalisa

Shugaban majalisar dattawan ya sanar da hakan ne a kaddamar da aiyukan majalisar wakilai na 2019 zuwa 2020.

Shugaban majalisar ya kara jaddada cewa 'yan majalisar bazasu lamunci kare kasafin kudin kowacce ma'aikata ko cibiyar gwamnati ba matukar ya wuce watan Oktoba.

Ya ce: "Ba zamu bar wani ya maida mana aikinmu baya ba. Muna kokarin ganin cewa mun amince da kasafin kudin 2020 kafin karshen shekarar nan. Duk wani minista ko shugaban cibiyar gwamnati da ya yi tafiya ko bai zo ya kare kasafin kudinsu ba, toh tabbas zamu aminta da kasafin ba tare da yayi hakan ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel