Dino Melaye:Yahaya Bello ya taya Adeyemi murnar samun nasara a kotun daukaka kara

Dino Melaye:Yahaya Bello ya taya Adeyemi murnar samun nasara a kotun daukaka kara

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayyana farin cikinsa a kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke game da zaben kujerar Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma inda ta yi watsi da zaben Sanata Dino Melaye.

A cikin shari’ar da kotun tayi a safiyar Juma’a 11 ga watan Oktoba, ta sake tabbatar da hukuncin kotun zabe inda ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta da ta sake gudanar da wani sabon zabe.

KU KARANTA:Shafukan sada zumunta na ba ‘yan sanda ciwon kai – IG Adamu

Yahaya Bello da Dino Melaye sun kasance abokan adawar juna a siyasance na tsawon shekaru uku kenan yanzu, wadanda a da kuwa suke karkashin inuwa guda ta siyasar.

Gwamnan a cikin wani zancen da mai magana da yawun bakinsa ya fitar, Mohammed Onogwu ya ce abinda kotun zaben ta fadi na cewa PDP ta tafka magudi a zaben ya tabbata yanzu.

Bello ya yabawa kotu a kan tsayawa a kan gaskiya ba tare da nuna son kai ba kuma rashin gaskiya a yayin yanke hukuncin.

Ga abinda zance yake cewa: “Duk da abubuwan da aka yita fadi game da hukuncin kotun zabe, na cewa ba daidai bane, sai ga shi kuma a yau kotun daukaka kara ta sake tabbatar da wannan hukuncin kamar yadda yake.

“Ina taya Smart Adeyemi murnar samun wannan nasarar a kotun daukaka kara. Gaskiyace kawai tayi halinta a wannan hukuncin ba komi ba, aikin gama ya riga ya gama yanzu kam.” Inji Bello.

https://www.premiumtimesng.com/regional/north-central/357136-governor-yahaya-bello-hails-judgement-sacking-melaye-congratulates-adeyemi.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel