Sojoji sun ceto daliban sakandare da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Sojoji sun ceto daliban sakandare da aka yi garkuwa da su a Kaduna

- Rundunar sojin 'Operation Thunder Strike' sun samu nasarar ceto daliban makarantar sakandare da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna

- Sojojin sun yi musayar wuta da 'yan ta'addar inda bayan sun ci karfinsu suka yadda makamai suka fada daji

- Yanzu haka dai sojojin sun samu nasarar ceto duka daliban da 'yan bindigar suka sace

Rundunar sojin 'Operation Thunder Strike' ta ceto daliban makarantar sakandare dake garin Gwagwada cikin karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna, wadanda aka yi garkuwa da su a makon da ya gabata.

A cewar rundunar sojin, sun kuma kashe 'yan bindiga guda hudu a wurare daban-daban sannan kuma sun samu nasarar kwace makamai masu hadarin gaske a wajen su.

Mataimakin darakta na jami'in hulda da jama'a na hukumar sojin, Colonel Ezindu Idima shine ya bayyana hakan a yau Juma'ar nan.

Ya ce a lokacin da rundunar take zagaye a yankin karamar hukumar Chikun din, sun samu rahoto cewa akwai wasu 'yan bindiga da suka hana mutane sakat a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, kuma har ma sun kama wasu dalibai da suke kan hanyar su ta zuwa makaranta.

KU KARANTA: An gano mutumin da ya fito a bidiyon da ake zargin Sheikh Daurawa ne

"A take a wajen sojojin suka bazama neman 'yan bindigar inda suka samu musayar wuta tsakaninsu, a karshe dai 'yan bindigar sun zubar da makaman su.

"Bayan tsagaita wuta an samu nasarar kama daya daga cikin 'yan bindigar inda sauran kuma suka ranta cikin daji ana kare da muggan raunika a jikinsu, kuma an samu nasarar ceto duka daliban da 'yan bindigar suka sace."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel