Jita-jitan auren Buhari da Sadiya: Masallacin Aso Villa ta cika yau

Jita-jitan auren Buhari da Sadiya: Masallacin Aso Villa ta cika yau

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma'a ya gabatar da Sallan Juma'arsa a masallacin fadar shugaban kasa, dake Abuja kamar yadda ya saba.

Daga cikin wadanda suka halarci Sallar tare da shi sune hadimansa, wasu ministoci, tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari da Sanata Kabiru Gaya.

Masallacin Juma'ar a yau ta samu baki da yawa ba kamar yadda aka saba gani ba. Jaridar The Nation ta bada rahoto.

Ana kyautata zaton cewa sun dira masallacin don su tabbatar da gaskiyar jita-jitan da ke yawo a kafafen ra'ayi da sada zumunta inda ake cewa shugaba Buhari zai dau sabuwar amarya yau.

Labaran bogin sun yi ikirarin ceewa shugaba Buhari zai auri ministar tallafi da manajin annoba, Hajiya Sadiya Umar Farouq.

Amma hakan bai faru ba a masallacin fadar shugaban kasa ranar Juma'a.

KU KARANTA: Yaro dan shekara goma sha ya yiwa yar shekara 50 fyade a Kano

Tuni dai hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman a kafofin watsa labarai, Mista Femi Adesina domin tabbatar da gaskiyar lamarin, inda shi kuma ya yi watsi da labarin. Adesina yace kawai yaudara ce daga wadanda suka kagi labarin na karya.

Ya bayyana cewa labarin ba komai bane face karya sannan kuma cewa babu wani batun aure makamancin haka da zai gudana a fadar Shugaban kasa a ranar Juma’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel