Shafukan sada zumunta na ba ‘yan sanda ciwon kai – IG Adamu

Shafukan sada zumunta na ba ‘yan sanda ciwon kai – IG Adamu

Sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu a ranar Juma’a 11 ga watan Oktoba ya ce wata babbar matsala da ke cima ‘yan sandan Najeriya tuwo a kwarya ita ce shafukan sada zumunta.

A cewarsa wannan matsala ce wadda ta jima tana cima ‘yan sanda tuwo a kwarya a daidai wannan lokaci.

KU KARANTA:Kudin makamai: Ya kamata Jonathan ya gana da Buhari a kan Dasuki – Sule Lamido

Adamu ya fadi wannan maganar ne a wani taron wayar da kai wanda aka shiryawa jami’an hulda da jama’a na hukumar dake jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja, a Aguu ta jihar Anambra.

Adamu ya ce: “Abubuwa sun riga sun sauya a yanzu, hanyoyin sadarwa gaba daya sun canza zuwa na zamani. Akwai kafofin isar da bayanai iri daban-daban a yau.

“Shafukan sadarwa na zamani kan iya gyarawa ko kuma lalata maku aiki. A matsayinku na jami’an ‘yan sanda aikinku shi ne kare mutuncin aikin dan sanda a ko da yaushe. Ba ko da yaushe ake bukatar buga bayanai a takarda ba.

“Yadda zamani yazo da sauki a yanzu zaku iya yin amfani da hanyoyin sadarwa na zamani ma. Amma dai yin amfani da ita ta hanya mafi dacewa shi ake bukata daga wajenku ba akasin hakan ba.” Inji Adamu.

Kari a kan jawabinsa, Adamu ya gargadin jami’an da su guji tankawa ga labaran karya da kuma jita-jita, inda ya ce wani lokaci ana yinsu domin a tayar da zaune tsaye.

“So tari masu kirkirar wadannan labaran mutane ne masu basira kwarai, a don haka sai kun yi amfani da gogewarku kuma wurin magance irin wannan matsala.” Inji Sufeto janar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel