Yaro dan shekara goma sha ya yiwa yar shekara 50 fyade a Kano

Yaro dan shekara goma sha ya yiwa yar shekara 50 fyade a Kano

Wata kotun majistare dake zaune a jihar Kano a yau Juma'a ta bada umurnin garkame matashi mai suna, Babangida Inusa, wanda ya yiwa mahaifiyar makwabcinsa yar shekaru 50 da haihuwa fyade.

Kotun ta ce a tsareshi a gidan maza kafin ta yanke shawara kan abinda za tayi masa. Sahara Reporters ta bada rahoto.

Jami'an yan sanda sun tuhumci Babangida Inusa wanda mazaunin garin Falgore, karamar hukumar Kabo na jihar Kano da laifin fyade.

Alkalin kotun, Muhammad Idris, ya ki sauraron jawabin Inusa, kawai ya umurci yan sanda su mayar da kararshi hukumar hukuntar masu laifi domin shawara.

Alkalin ya dage karar zuwa ranar 12 ga Disamban 2019 domin cigaba da sauraro.

Alkalin gwamnati, ASP Badamasi Gawuna, ya bayyanawa kotu cewa dan matar mai suna Rabiu Hussaini ne ya kawo karar matashin ofishin hukumar dake Garo.

Gawuna ya ce Babangida Inusa ya zakkewa mahaifiyarsa ne a gonarta dake karamar hukumar Kabo.

KU KARANTA: Shikenan, kotu ta kwace kujerar Sanata Dino Melaye

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Firam ministan kasar Habasha (Ethiopia), Abiy Ahmed, murnan samun kyautar Nobel na zaman lafiya.

A yau, Kwamitin Nobel ta Royal Swedish Academy ta baiwa Abiy Ahmed lambar yabon Nobel sakamakon sulhun da yayi tsakanin kasarsa da kasar Eriteriya bayan shekaru 20 da aka kulla gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel