Kudin makamai: Ya kamata Jonathan ya gana da Buhari a kan Dasuki – Sule Lamido

Kudin makamai: Ya kamata Jonathan ya gana da Buhari a kan Dasuki – Sule Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya roki tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan na ya sanya baki cikin lamarin Sambo Dasuki, tsohon mai bada shawara ga shugaban kasa game da tsaro.

Lamido ya ce ya kamata Jonathan ya yiwa Buhari magana domin a sako Sambo Dasuki wanda aka tsare tun shekarar 2015. Ana zargin Dasuki da yin sama da biliyan N19.4 kudin makamai.

KU KARANTA:Farin ciki ya game gari a wata jihar kudu bayan Gwamnansu ya ce zai biya mafi karancin albashi a karshen Oktoba

Amma sai dai Sule Lamido na ganin babu adalci cikin wannan lamarin, kasancewar shugaban CBN, Godwin Emefiele wanda da saninsa aka fitar da kudin na nan zamansa babu abinda aka yi masa.

Jonathan din dai ya gana da Shugaba Buhari a wani zama na sirri inda suka ja labule a Villa ranar Alhamis 10 ga watan Oktoba, 2019.

Da yake tsokaci game da ganawar, Lamido yayi amfani da shafinsa na Facebook inda yayi magana a kan abinda ya faru a wancan lokacin. Lamido ya fadi cewa ba Dasuki kadai ba ne ke da laifi, inda ya ce mutum uku ne, Dasuki, Emefiele da Jonathan.

Sule ya ce: “Na tabbata duk abinda ya faru a lokacin cire kudin Jonathan ne yayi sila, saboda duk yadda ya ba Dasuki umarni ba zai iya cewa a’a ba saboda matukar biyayyar da yake masa. Haka kuma Emefiele ba zai bada kudi ba said a izinin Jonathan.

“Ko shi kan shi Shugaba Buhari ya fadi da bakinsa cewa daga CBN aka fidda kudin a cikin wani zancen da aka rubuta a karamar takarda.” A cewar Lamido.

https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/357127-why-jonathan-should-speak-with-buhari-over-dasuki-sule-lamido.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel