Farin ciki ya game gari a wata jihar kudu bayan Gwamnansu ya ce zai biya mafi karancin albashi a karshen Oktoba

Farin ciki ya game gari a wata jihar kudu bayan Gwamnansu ya ce zai biya mafi karancin albashi a karshen Oktoba

-Kayode Fayemi na shirin biyo sahun Kaduna da Kebbi wurin kaddamar da biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikata

-Gwamnan ya fadi wannan maganar ne a wurin taron ranar malamai ta duniya a Ado Ekiti babban birnin jihar ta Ekiti

Yayin da maganar mafi karancin albashin ke cigaba da zagaye a Najeriya, wani gwamnan APC a daya daga cikin jihohin Kudu maso Yamma ya bayyana aniyarsa ta soma biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi a karshen watan Oktoba.

Kayode Fayemi, Gwamnan jihar Ekiti yayi wannan alkawarin ne a wurin taron bikin ranar malamai ta duniya a filin wasanni na Oluyemi Kayode dake Ado Ekiti, ranar Asabar 5 ga watan Oktoba, 2019.

KU KARANTA:Zaben Shugaban kasa: CUPP na zargin akwai munakisa da aka shiryawa karar Atiku a Kotun koli

Gwamnan ya ce fara biyan mafi karancin albashi ne a matsayin wata hanya ta farantawa ma’aikatansa rai musamman malaman makaranta a jihar.

Fayemi ya sake bada tabbacin cewa karin albashin zai karawa musamman malaman makaranta kwarin gwiwa ta yadda za su rinka koyar da daliban yadda ya kamata.

Haka zalika, gwamman yayi amfani da wannan taron domin karrama malamai mafiya hazaka daga wasu makarantun jihar Ekiti. Malaman da aka karrama su hada da; Henry Olaoluwa Asubiojo na Amoye Grammar School, Tajudeen Olaoye na Anglican Primary School da Mojisola Ehinafe na Technical School.

Ko wanne daga cikin malaman kyautar naira 500,000 ya tafi da ita gida a ranar daga hannun Gwamna Kayode Fayemi.

Da yake bayyana cigaba da ya kawo a bangaren ilimin jihar Ekiti, Fayemi ya ce ya dauki karin malamai 2,000 aiki a makarantun gwamnatin jihar.

Haka kuma ya tsiri gina karin makarantu domin rage cinkoso a makarantun gwamnatin jihar da suka riga suka cika makil da yara masu zuwa neman ilimi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel